23 Maris 2020 - 13:41
An Kafa Dokar Hana Yawo A Saudiyya Saboda Cutar Corona

Sarkin Saudiyya Salman Bin Adbulaziz ya sanar da kafa dokar rage kai da komowa a fadin kasar wacce za ta fara daga karfe 7;00 na marecen kowace rana zuwa karfe 6;00 na safiya, har tsawon kwanaki 21.

(ABNA24.com) A yau Litinin ne dai ake sa ran cewa dokar za ta fara aiki, kamar yadda kamfanin dillancin labarun Saudiyya ya nakalto.

Sai dai dokar ta yi togiya akan muhimman cibiyoyi na gwamnati da masu zaman kansu da su ka hada na tsaro,kiwon lafiya, kafafen watsa labaru da sauran cibiyoyi masu matukar muhimmanci.

Bugu da kari sanarwar ta bukaci ‘yan kasar ta Saudiyya da su zauna a cikin gidajensu, kada su fito waje sai idan bukata mai tsanani ta taso.

Saudiyyar dai ta hana yin taruka da haduwar mutane, da su ka hada da wuraren ibada har da masallatan Makka da Madina.

342